Labarai
Ranieri ya zama Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Watford
Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta sanar da nada Claudio Ranieri a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasan kungiyar, domin maye gurbin Xisco Munoz wanda ta sallama a ranar Lahadi.
Dan kasar Italiya, mai shekaru 69 ya koma horas da ‘yan wasa a gasar a Primiyar kasar Ingila ne, bayan rawar da ya taka a Leicester City a tsakanin shekarar 2015 da 2016, wanda ya bar Sampdoria tun kan fara kakar wasanni ta bana.
Claudio Ranieri shine mai horaswa na goma 14 da kungiyar ta Watford ta dauka tun bayan da iyalan Pozzo suka mallaki kungiyar a shekar 2012.
An umarci Ranieri da ya bunkasa wasannin kungiyar da take fafatawa a gasar Primiyar kasar Ingila, wadda take ta 14 a kasan teburi da maki bakwai bayan data buga wasa bakwai.
Wasan farko da Ranieri zai jagoranci kungiyar shine wanda za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Asabar 16 ga watan da muke ciki.
Masana harkokin kwallon kafa a kasar Ingila na ganin Ranieri yana da gogewar da zai iya daga martabar Watford.
You must be logged in to post a comment Login