Labaran Kano
Rashin amincewa da COVID-19 ya sanya yaduwar cutar-Masani
Wani masanin tattalin arziki dake kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano Dr Gazali Ado, ya bayyana ta’azzarar yaduwar annobar COVID-19 da cewa, ta faru ne sakamakon rashin daukar cutar da muhimmanci daga wasu shugabanni farkon bullarta.
Dr Gazali Ado, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis ta cikin Shirin “Duniyarmu a Yau” nan Freedom Radio wanda ya mayar da hankali kan tattalin arziki da tsarin zamantakewa.
Malamin ya ce, cuta ce mai matukar hatsari, sai dai wasu mutanen sun dauketa da wasa inda har ma ya buga misali da shugaban Amurka Donald Trump.
Haka kuma ya bayyana cewa, akwai wasu cutuka da suka hallaka al’umma a fadin duniya, amma ba su kai irin yadda ake samun matsala a halin yanzu ba, kasancewar yanzu haka tattalin arzikin duniya ya samu matsala.
Shi kuwa Alhaji Fu’ad Hassan na kungiyar dattawan Kano ta KCCI, da ya kasance a cikin shirin ya bukaci mutane kan su rika kare kansu daga duk wata hanya da ke a matsayin wadda za ta sanya a kamu da kwayar cutar ta Corona.
Ya kuma bukaci mutane da su tabbatar da cewa, suna bin umarnin jami’an lafiya a kokarinsu na magance yaduwar wannan annoba.
You must be logged in to post a comment Login