Labaran Wasanni
Rashin Kabiru Baleriya Babban gibi ne a harkokin wasanni -SWAN
Kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kano, ta bayyana rasuwar Kabiru Baleriya, a matsayin wani gibi da za’a dade ba a cike shi ba.
Shugaban kungiyar na Kasa Honour Sirawoo, ne ya bayyana haka wanda ya samu wakilcin mataimakin sa na yankin Arewa maso yamma, kuma kakakin kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars Rilwanu Idris Malikawa, wanda ya jagoranci tawagar marubutan zuwa ta’aziyya gidan mamacin a madadin shugaban.
Honour Sirawoo, ya ce Baleria hazikin dan Kwallo ne lokacin da yake murza Leda, kuma ya kasance mai kwazo kwarai da gaske lokacin da yake mai horar wa, don haka munyi rashin dan uwa daga cikin mu.
Muna fatan Allah yaji kansa, muna kuma baiwa iyalan sa hakurin jure rashin sa a madadin mu da duk abinda ya shafi harkokin wasanni na kasa.
Karin labarai:
Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu
Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana
Suma a nasu bangaren kungiyar masu horar da yan wasa, karkashin jagorancin Ladan Bosso, ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan dan wasan ta hannun mataimakin mai bada horo na kasa na kungiyar Danlami Usman Akawu, wanda ya wakilci shugaban.
Ladan Bosso, ya ce ba za a manta da Baleria ba, kasancewar sa ya bautawa kasar nan ta hanyar buga mata wasanni, tare da bada gudunmowar sa ga bunkasa wasan a fannin koyar dashi.
Muna fatan iyalin sa , za suyi hakuri da wannan Babban rashi.
Ita ma, kungiyar kwallon kafa ta Elkanemi Warriors dake garin Maiduguri, karkashin jagorancin kungiyar magoya bayanta, ta kai makamanciyar irin wannan ta’aziyya, tare da Addu’a ga mamacin da iyalan sa.
A lokacin da ya na raye kuma yana taka Leda, Kabiru Baleriya, ya wakilci kungiyar kwallon kafa ta Elkanemi Warriors da kungiyoyi da dama.
Kabiru Baleriya, ya rasu a yammacin Talatar data gabata, bayan fama da rashin lafiya da yayi.
You must be logged in to post a comment Login