Labaran Wasanni
Rashin kyan filaye ne ke kawo nakasu ga ‘yan wasa – Joseph Yobo
Mataimakin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Joseph Yobo, ya ce ‘yan wasan dake buga gasar Firimiya ta kasa, na bukatar filin wasa na zamani mai kyau ta yadda za su iya nuna irin hazakar da suke da ita yadda ya kamata.
Yobo ya kuma ce hakan ne zai sanya a gane irin kwazon da yan wasan suke da shi ta yadda za’a iya gayyatar wasun su zuwa babbar tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles domin bayar da tasu gudin mawar.
Joseph Yobo ya kuma ce a wannan lokacin kungiyar ta super Eagles zata baiwa ‘yan wasan dake wasa a cikin gida damar shigowa tawagar yadda ya kamata,
A wani kokari da kasar nan keyi domin rage yawan amfani da ‘yan wasan dake wasa a kasashen turai a kungiyar ta Super Eagles.
Ya kuma ce rashin kyawun filin wasa ga yan wasan kasar nan na daya daga cikin abin da ke kawo nakasu, wajen nuna irin hazakar da ‘yan wasan suke da itah.
Joseph Yobo ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da tsohon mai magana ya yawun kungiyar ta Super Eagles, Colin Udoh a birnin tarayya Abuja.
A kwanakin baya dai hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta gindaya sharudan cewa za’a rinka amfani da ‘yan wasan dake wasa a cikin gida a kungiyar kwallon kafar ta kasa Super Eagles.
Hakan na kunshe cikin sharudan data baiwa mai horar da kungiyar Gernot Rohr kafin ta amince ta kara masa sabon kwantaragin shekaru biyu na ci gaba da jagorantar ‘yan wasan kasar nan zuwa nan da shekara ta 2022.
You must be logged in to post a comment Login