Connect with us

Labaran Wasanni

Iyaye su rinka fadakar da ‘yayansu illar Fyade- Ogenyi Onazi

Published

on

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Ogenyi Onazi, ya buka ci iyaye a kasar nan da su rinka wayar da kan ‘ya’yan su Maza kan illar da yin Fyade ga ‘ya’ya mata yake da shi.

Onazi, ya ce a ‘yan kwanakin nan an samu yawan aikata Fyade ga ‘ya’ya mata a kasar nan wanda ya janyo da yawa daga cikin al’ummar kasar nan ke takaicin yawan samun matsalolon na Fyade a wannan lokacin.

Ya kuma ce matsalar Fyade na daya daga cikin abin da ke kawo masifa a kasa ta yadda masifu ke afkuwa a gurare daban daban a kuma rasa musabbabun abin da ya kawo su.

Onazi ya kara da cewa yakan ji bakin ciki a duk lokacin da ya samu labarin wani yayiwa wata fyade a kasar nan.

A don haka yake kara kira ga malamai da gwamnatoci da iya’ye kan su rinka gudanar da wani shiri na musamman a makarantun kasar nan da zai rinka wayar da kan mutane kan illar da fyade yake dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,980 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!