Labarai
Rashin magance kananan cututtuka shine ke kawo manya -Likita
Shugaban sashen nazarin lalurar koda na asibitin koyarwa na Aminu Kano Saminu Muhammad ya ce, rashin magance kananan cututtuka da ke addabar al’umma da wuri na daga cikin dalilan dake kara haddasa yaduwar manyan cututtuka ga mutane.
Malam Saminu Muhammamd, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsin na nan tashar freedom rediyo wanda ya mayar da hankali kan ciwon Koda.
Ya ce, cututtuka irin su hawan jini da amai da gudawa da kuma ciwon siga suna daga cikin lalurar da ke haifar da ciwon Koda.
LABARAI MASU ALAKA
Cutar ciwon kunne na raguwa sakamon wayar da kan al’umma- Likita
Asalin cutar Tamowa na afkuwa ne tun kafin a haifi jariri- Likita
AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu
A nasa bangaren wani malamin jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Malam Mustapha Adam ya ce, kamata ya yi duk mutumin da ya ke dauke da wannan lalura, ya san irin abubuwan da ya kamata ya rika yi don kare kansa daga kara ta’azarar cutar.
Bakin dai sun kuma yi kira ga jama’a da su rika ziyartar asibiti akai-akai don yin gwaji, ba lallai sai sun ji basu da lafiya ba
You must be logged in to post a comment Login