Connect with us

Kiwon Lafiya

Akwai barazanar kamuwa da cutar sukari saboda rashin wasu sinadarai – Likita

Published

on

Daga Safarau Tijjani Adam

 

Farfesa Ibrahim Danjummai ya ce rashin samun wasu sinadarai a jikin mutum na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa ciwon suga a jikin dan adam.

Kwararren likita a sashen kula da masu ciwon suga wato Diabetes da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano ne ya bayyana ta cikin shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom Radio.

Ya ce ko wane mutum zai iya kamuwa da ciwon suga, musamman yadda a yanzu ciwon ke kama kananan yara.

Farfesa Ibrahim Danjummai na yin wannan jawabi ne a wani bangare na bikin ranar masu fama da ciwo suga ta duniya.

Ita kuwa jami’ar jinya a asibitn koyarwa na Aminu Kano Hajiya Hauwa Ibrahim ta ce rashin motsa jiki na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ciwon suga.

Jami’an biyu sun shawarci jama’a da su rinka zuwa asibiti ana duba lafiyarsu a ko da yaushe domin sanin matakin lafiyarsu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!