Labaran Kano
Rashin sanya hannu Kan dokar Kare hakkin Kananan Yara ne yasa suke fuskantar cin zarafi: FIDA
Kungiyar Mata Lauyoyi ta Duniya FIDA ta ce, rashin sanya hannu Kan dokar Kare hakkin Kananan Yara da gwamnatocin kasar nan basuyi ba, shine yasa Yara ke Kara fuskantar cin zarafi a halin yanzu.
Shugabar kungiyar ta kasa reshen Jihar Kano Barrister Bilkisu Ibrahim Sulaiman ce ta bayyana hakan a zantawar ta da Freedom Radio Kan makon Lauyoyi na Duniya da kungiyar ta gabatar.
A Rana ta Farko 26 ga watan Yunin shekarar 2024 kungiyar ta FIDA ta Kai ziyara gidan Yara Marayu dake Nasarawa, inda ta dubasu tare da Kai musu kayyakin Tallafi haka Kuma a ranar dai ta Kai ziyara gidan Yara na Torry Home dake Tudun Maliki inda nan ma ta Tallafa musu da kayan ciye ciye da kuma na amfanin yau da kullin.
Haka zalika kungiyar ta kaiwa Babban jojin jihar Kano ziyara a dai ranar.
Kazalika kungiyar a washegari ta gabatar da taro na musamman kan yadda mutanan da akaci zarafin su musamman Kananan Yara za su Kai koken su ga hukuma.
Taron makon kungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya FIDA dai ya samu halartar shugabar kungiyar a nan Najeriya da membobin ta dake Jihohin kasar nan daban daban.
Shugabar kungiyar Lauyoyi ta Duniya FIDA reshen Jihar Kano a nan Najeriya Barrister Bilkisu Ibrahim kenan.
You must be logged in to post a comment Login