Labarai
Rashin shugabanci ya janyo harkar fim ta faɗi ƙasa warwas – Falalu ɗorayi
Darakta kuma mai bada umarni a masana’antar Kannywood ya ce, tuni harkokin masana’antar suka faɗi ƙasa warwas dalilin rashin kyakkyawan shugabanci.
Falalu Ɗorayi ne ya bayyana hakan yayin gabatar da wani shiri na musamman da Freedom Radio ta yi kan masana’antar a ranar Asabar.
Ɗorayi ya ce, tun lokacin da aka daina buga fina finan a kaset da kuma CD harkar ta samu koma baya.
“Mafi yawa daga cikin masu shirya fina-finai ko ɗaukar nauyin sa, tun a wancan lokaci al’amuran su suka tawaya, domin kuwa wasu basu da ƙudin da za su kai fim ɗin su sinima a haska ko ɗaukar nauyin sa a gidan talabijin wanda a yanzu su ne hanyoyin da ake cin kasuwa fim” in ji Falalu Ɗorayi.
Sai dai ya ce, ta wannan hanya ce aka samu ci gaba a masana’antar tsawon shekaru, har ma ya ƙara cewa duk da ana sakin fina-finan ta manhajar YouTube, amma babban ƙalubale ne a ɓangaren, domin kuwa anan masu satar fasaha ke cin karen su babu babbaka.
“Kasuwancin fim da ma shirya fina-finan za mu iya cewa a yanzu ba a yi, sakamakon rashin masu shiryawa da bada umarni har ma da jaruman” a cewar Ɗorayi.
Falalu Ɗorayi ya ɗora alhakin matsalolin da Kannywood ke fuskanta akan rashin shugabanci mai kyau, wanda ya ce, mafi yawa daga cikin ƴan ƙungiyar sun koma wasu jihohin don ci gaba da ayyukan su.
You must be logged in to post a comment Login