Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Rashin tsari ne ya kara tabarbare bangaren ilimi a Najeriya – Masani

Published

on

An bayyana cewa rashin tsari ne ya janyo tabarbarewar ilimi a wannan lokaci da duniya ke fuskantar annobar corona.

Dakta Abubakar Sadiq Haruna na tsangayar ilimi ta jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan tashar Freedom Rediyo da ya mayar da hankali kan hana bude makarantu da Gwamnatin tarayya ta yi.

Ya ce, a shekarun 1956 zuwa 1957 an samu irin wadannan matsaloli da suka dakatar da harkoki a duniya, sai dai, kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da fasahar zamani wajen inganta harkokin ilimi a kasar nan.

Dakta Abubakar Sadiq ya kara da cewa wannan matakin zai iya jawowa dalibai nakasu a iliminsu da kuma irin tunaninsu ta yadda shawo kan mastalar na iya kawo koma baya a bangaren malamai a makarantu.

Ita ma shugabar kungiyar makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano, Hajiya Maryam Muhammad cewa ta yi umarnin na gwamnati ya taba makarantu masu zaman kansu ta bangarori da dama musamman ma ta fuskar kudaden biyan malamansu albashi.

Bakin biyu sun bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su samar da matakai na sosai a bangaren ilimi don magance barazanar da ilimi ke fuskanta a halin yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!