Connect with us

Kaduna

Rashin tsaro: An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana dokar takaita zirga-zirga na tsawon sa’o’i 24 a ƙananan hukumomin Jema’a da Kauru.

Wannan dai ya biyo bayan shawarar da hukumomin tsaro a jihar suka bayar don inganta tsaro a yankunan.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Samuel Aruwan ya fitar ta ce, sanya dokar taƙaita zirga-zirgar zai baiwa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukan su na wanzar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka kuma jami’an tsaro za su sanya ido don ganin al’ummar yankunan su bi dokar.

Sanarwar takuma buƙaci su da su baiwa jami’an tsaron haɗin kai wajen gudanar da ayyukan su domin dawo da zaman lafiya a yankunan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!