Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin tsaro ne babban ƙalubalen da gwamnatin Buhari ta fuskanta a 2021 – Lai Muhammad

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce rashin tsaro ne babban ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar 2021.

Ministan yaɗa labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan yau, yayin taron manema labarai a Abuja.

Lai Muhammad ya yi tsokaci kan nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu a bana.

Daga cikin nasarorin da gwamnatin tarayya ta samu har da hallaka ‘yan ta’adda sama da dubu ɗaya da sojojin ƙasar nan suka yi tare da ceto rayukan mutane dubu biyu.

Sai kuma yadda wasu ‘yan ta’adda sama da dubu ashirin da biyu da suka ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga jami’an tsaro a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!