Labarai
Rashin wuta: Matan unguwar Medile sun gudanar da zanga-zangar lumana
Matan unguwar “Cika Sarari” da ke Medile a ƙaramar hukumar Kumbotso anan Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana.
Zanga-zangar ta su, sun yi ta ne domin nuna fushin su kan rashin hasken wutar lantarki da suke fama da shi tsawon lokaci.
Da yammcin Talata ne matan suka fito zanga-zangar daga cikin gidajen su tare da zagaye unguwar a wani mataki na bayyana halin da suke ciki.
Hafsa Aliyu Hamza ita ce ta wakilci matan ta ce “Mun fi shekara 7 muna fuskantar rashin wuta, wanda kuma ɓata gari ke samun mafaka suna cin karen su babu babbaka”.
“Ba ma fita da magriba saboda yadda wasu mutane suke laɓewa a cikin ciyayi suna yi mana barazana dalilin kenan da ya sa muka fito zanga-zanga don mahukunta su san halin da muke ciki” a cewar Hafsa.
Shi ma ɗaya daga cikin mazajen matan mai suna Safiyanu Ali Sani ya ce “Mu muka amincewa matan mu su gudanar da zanga-zangar domin kuwa su suke fuskantar matsala fiye da mu, ga sauro da zafi”.
Safiyanu ya ci ga da cewa “ Wani dan majalisa ya ba mu taransifoma amma haɗata har yanzu ya gagara domin kuwa har yanzu kuɗaɗen da ake buƙata domin haɗata ba su samu ba”.
Al’ummar unguwar sun yi fatan mahukunta su kawo musu ɗauki don fitar da su daga halin da suke ciki.
You must be logged in to post a comment Login