Sharhi
Rikicin Aisha Buhari da mukarraban Shugaban kasa: Yaushe wuta zata tsagaita?
Tun a shekarar 2016 ne uwargidan shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta fara bayyana rashin jin dadin ta game da wadanda ta bayyana ’yan bani na iya suka hana ruwa gudu a gwamnatin da mijinta kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.
Aisha Buhari wacce a yanzu shekaru talatin kenan da suka yi aure da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan rabuwar da yayi da marigayiya tsohuwar uwargidan sa Hajiya Safinatu ta cigaba da kin boye abunda ke damun ta game da yadda wasu ke katsalandan a tafiyar da al’amuran na Najeriya.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun banbanta akan irin yadda maidakin na shugaban kasa ke bayyana ra’ayinta a game da tafiyar da gwamnati da shugaba Muhammadu Buhari ke yi , inda wasu ke ganin cewa tayi dai dai da bayyana rashin jin dadinta da kuma kokarin kawo gyara.
Amma wasu na ganin duba da yadda al’ada da addinin mutanan arewacin kasar nan yake, bai kamata Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta rika bayyana gazawar mijinta a kafafan yada labarai ba domin ita mace ce da ta ke da aure wanda matan musulmi basa bayyana a bainar jama’a sai hakan ya zama dole.
Ko a shekarar 2016 da Aisha Buharin ta nuna cewa wasu ne suka karbe ragamar mulkin Najeriya suke yin abunda suke so , bayan bayyanar bayanan nata a kafar yada labarai ta BBC sai da aka tambayi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yaya zai bayyana mai dakinsa.
Tunda cikin harshen turanci ya bayar da misalin sai shugaba Buhari yace shi dai abunda ya sani tsakanin sa da mai dakin sa shi ne tana dakinsa da gurin dafa abinci da kuma wani dakin daban.
Hakan yasa jama’a da dama suka rika mamakin na martanin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar akan caccakar da matar sa tayi wa gwamnatin ta sa.
Duk da haka tun fara dambarwar ,Shugaba Muhammadu Buhari bai taba mayarwa da Aisha Muhammadu Buhari martani akan caccakar da take yi na salon tafiyar da mulkin nasa ba.
Tun sanda ta fara ganin al’amura basa tafiya daidai a gwamnatin ta Shugaba Buhari wanda ita Hajiya Aisha take ganin talakawa ne suka sha wahala wajen samun nasara amma wasu ‘yan tsiraru suka mamaye da karbe iko kuma take ganin cewa talakawan basu amfana ba ko kadan.
Akwai ma wasu lokuta da Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa asibitin dake fadar shugaban kasa babu cikakkun kayan aiki da zai kula da marasa lafiya ballantana sauran asibitocin kasar nan.
Tarihin bayyanar Aisha Buhari
‘Yan Najeriya sun fara ganin Aisha Muhammadu Buhari ne a zaben shekarar 2015 lokacin da shugaba Buhari ya amince da ta shiga yakin neman zaben sa .
Amma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2003 da 2007 da 2011 ’yan Najeriya da dama da kuma magoya bayan shugaban basu san Aisha Muhammadu Buhari ba har sai lokacin zaben shekarar 2015.
Abunda ya bullo a satin nan
Kwatsam a ranar larabar da ta gabata sai ga shi uwargidan shugaban kasa ta zargi mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na musammman akan harkokin yada labarai da fuska biyu wajen gudanar da ayyukan sa.
Aisha Buhari ta bayyana cewa Malam Garba Shehu yana bin umarnin Mamman Daura ne ba na mijinta ba.
A zargin da tayi tace Mamman Daura ya umarci Garba Shehu da cire ‘’yan jaridun da suke aiki a ofishin mai dakin shugaban kasa da aka fi sani da First lady.
Yaushe rikicin zai tsagaita?
Har ya zuwa yanzu babu wani bangare a fadar Shugaban kasa ko shi Malam Garba Shehu ko Mamman Daura da ya mayar da martani.
Ko wane dabaru shugaba Buhari zai dauka na takaita maganar da ta shafi tafiyar da mulki da maidakin sa take yi ga manema labarai a shekaru uku da suka wuce.?