Labarai
Rikicin siyasa : Yadda kotu ta bada umarnin kama shugaban karamar hukuma a Kano
Kotun Majistire mai zamanta a garin Gezawa karkashin jagorancin mai sharia’a Salisu Haruna Bala, ta bai wa rundunar ‘yan sandan Jihar Kano umarnin kama shugaban karamar hukumar Gaya Ahmad Tashi Abdullahi da shugaban Kansiloli na Gaya Shu’aibu Mai Gado Gamarya a duk inda suke.
Tunda farko masu neman takarar shugabancin karamar hukumar Gaya guda bakwai ne suka shigar da kara a gaban kotun, sakamakon zargin dukan kawo wuka da suke zargin shugaban karamar hukumar da shugaban kansiloli na Gaya sun yi wa mutane biyu daga cikinsu a wajen tantancewa a ranar laraba 11 ga watan Nuwanban da muke ciki.
A yayin zaman kotun na yau mai shari’a Salisu Haruna Bala ya saurari dukkan bangarorin biyu, bayan kammala sauraron ne kuma nan take ya baiwa DPO na Gaya da na Gezawa umarnin kamo wadanda ake zargi da aikata laifin domin dankawa Kwamishinan ‘yan sanda na Kano, don ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
You must be logged in to post a comment Login