Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kotu : Dalilan da ya sanya za’a mai da ‘yan matan dake rawar salo gaban iyayen su

Published

on

Kotun shariar musulunci ta Ajingi , kar kashin mai sharia Malam Usman Haruna Tudun Wada, ta bada umarnin ma yarda wasu ‘yan mata dake rawar Solo biyu da aka kama gaban iyayensu saboda daya daga cikinsu na dauke da cutar HIV.

Wadanda ake zargin su da’yan asalin jihar Jigawa sun zo Kano ne domin yin Rawar Solo a wani killataccen guri a karamar hukumar Ajingi suna karbar Naira dari biyar ga duk wanda zai shiga don ya yi kallon  rawar badalar ta Solo.

Wadanda ake zargin sun hada da Bilyamin Haruna wanda shine ya yi musu jagoranci zuwa nan Kano domin su yi rawar Solo a karamar hukumar ta Ajingi sai Amina da kuma Sa’adatu.

An kuma karantowa wadanda ake zargi da laifukan da ake tuhumarsu sun kuma amsa, Inda mai sharia ya bada umarnin kai matan Asibiti domin a yi musu gwajin lafiyarsu nan take kuma Likita ya  tabbatar da cewa guda daga cikin ‘yan matan biyu na dauke da cutar kanjamau.

Wakilin mu Abdulkarim Muhd Tukuntawa ya ruwaito cewa  mai sharia Usman Haruna ya yankewa Bilyamin hukuncin daurin watanni biyu babu zabin tara a gidan gyaran Hali an kuma tsula masa bulala Hamsin nan take don ladabtar da shi.wwwww ccaw1qa1a

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!