Labarai
Rundinar Yan Sandan Kano ta yi nasarar cafke ‘yan Sandan bogi

Kakakin rundinar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya shaida hakan a wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na Facebook, ya ce, an kama mutanen da kayyaki ciki har da katin aiki ‘yan sanda na bogi , da ankwa ,da kudi na CFA 2,500, da kudin Najeriya harma da motarsu kirar Fijo 406 mai launin shuɗi wadda ke da lambar rijista NSR-189-BD.
Wadanda aka kama sun hadar da:
Aliyu Abbas, mai shekara 35, Sani Iliyasu, mai shekara 47, Ashiru Sule, mai shekara 41, Abubakar Yahaya, mai shekara 45 sai Adamu Kalilu, mai shekara 45.
A yayin bincike, wadanda ake zargin sun amince da laifinsu, inda suka bayyana cewa suna amfani da katin aikin ‘yan sanda na bogi don karɓar cin hanci da zaluntar jama’a a jihohin Kano, Katsina da Kaduna. Rundinar ta ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
You must be logged in to post a comment Login