Labarai
Rundunar ƴan sandan na shirin ci gaba da bada Tinted Permit

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya, ta sanar da cewa za a ci gaba da bada izinin mallakar gilashi mota mai-duhu,wato tinted, daga 2 ga watan Janairu mai kamawa.
Rundunar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’inta na hulda da jama’a na ƙasa Benjamin Hundeyin ya sanya wa hannu.
Ta cikin sanarwar Benjamin ya ce, bada izinin ya biyo bayan nazari sosai kan matsalolin tsaro da suka kunno kai da kuma bukatar tabbatar da tsaron ga ‘yan kasa.
Sanarwar ta kuma ce, babu wani umarnin kotu da ya hana ‘yan sanda aiwatar da doka kan bakin gilashin na tinted.
You must be logged in to post a comment Login