Labarai
Rundunar sojan kasar nan ta bukaci rufe offishin kungiyar Amnesty international
Rundunar sojan kasar nan ta yi kira da a rufe offishin kungiyar Amnesty International dake kasar nan, yayin da take zargin da akwai kwararan hojoji kan kungiyar na kokarin tarwatsa Najeriya.
Mai Magana da rudunar Birgediya Janaral Sani Usman Kuka-Sheka ya sanar da hakan, cewa kungiyar na kokarin tarwatsa kasar nan wajen yada kalaman karya na zargin hukumomin tsaron kasar nan na take hakin al’umma.
A cewar sa, reshen kungiyar ta Amnesty International dake kasar nan ya sauka daga kan gwadabe, na kudorori da manofofin da aka san shi da shi dake da shelkwata a Burtaniya, wajen raraba kawunan ‘yan Najeriya shekaru da dama ta amfani da rikicin kungiyar Boko Haram da na mabiya darikar shi’a da kuma na rikicin manoma da makiyaya.
Mai Magana da yawon rundunar sojan kasar nan ya kara da cewar, kungiyar na fitar da bayanai da rahotanni dake sokar lamirin rundunar sojan kasar nan kan ayyukan da suke yi don tada rikici da hautsani a tsakanin ‘yan Najeriya. Wannan shine karo na farko da rundunar sojan kasar nan ta nemi da a rufe ofishin kungiyar Amnesty International a Najeriya