Labarai
Rundunar Soji ta musanta labarin kai hari barikin sojoji a Borno
Rundunar Sojin kasar nan ta musanta labarin kai mata hari a Barikin Maimalari dake jihar Borno, da aka ce ‘yan Boko Haram sanye da kayan Majalisar Dinkin Duniya, sun kai mata da safiyar jiya Asabar cikin wani labari da aka rika yadawa a kafafen sada zumunta.
A wata takarda mai dauke da sa hannun Kanal Sagir Musa, mukaddashin kakakin Rundunar Sojin kasar nan, da aka rabawa manema labarai, tace wasu marasa kishin kasa da yada labaran karya, sun yi amfani da hotunan atisaye tsakanin Rundunar Sojin kasar nan na sashen aikin gudanar da tsaron LAFIYA DOLE, da na bangaren agajin tsaro na Majalisar dinkin duniya da ya gudana, wajen kara rura wutar labarin Kanzon Kuregen, don tayar da hankalin jama’a da kuma saka shakku da rudani.
Don haka Rundunar a cikin sanarwar ta ke shaidawa al’umma cewar ba kamshin gaskiya a labarin, kuma babu wani tasgaro na tsaro a Barikin na Maimalari ko cikin birnin Maiduguri.
Don haka jama’a suyi watsi da labarin.
Karin labarai:
An dambata tsakanin KAROTA da Sojoji
Sanarwar ta kara da umartar al’umma dasu cigaba da gudanar da harkokin su yadda aka saba, kasancewar Rundunar samar da tsaron ta LAFIYA DOLE, a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar nan musamman ma wanda suke a yankin da take gundanar da aikinta.
Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga al’umma da su dau halayyar tan-tance sahihan labarai da na karya, don kaucewa shiga rudani, da abinda ya shafi al’umma.
You must be logged in to post a comment Login