Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojin kasar nan da ta kasar Amurka zasu gudanar da wani taron a Abuja

Published

on

Rundunar sojin kasa na kasar nan tare da hadin gwiwar takwaranta ta kasar Amurka da ke kula da nahiyar afurka, za su gudanar da wani taro na rundunar sojin kasa na Afurka a birnin tarayya Abuja daga ranar Litinin sha shida ga wata zuwa Alhamis sha tara ga wata.

Shugaban sashen ba da horo na rundunar sojin kasa na kasar nan, Burgediya Janar David Ahmadu ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce za a tattauna batutuwa da dama ciki har da yaki da kungiyar ISIS da kuma hatsarin ta ga nahiyar afurka.

Burgediya Janar David Ahmadu ya kuma ce taron zai taimakawa manyan hafsoshin soji da ke nahiyar afurka wajen aiki tare domin fuskantar kalubalen ‘yan ta’adda.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!