Kiwon Lafiya
Rundunar sojin kasar nan ta ce ta na cigaba da barin wuta a dajin Sambisa
Rundunar Sojin kasar nan ta bayyana cewa ta na cigaba da barin wuta a dajin Sambisa a wani bangare na cigaba da tarwatsa mayakan Boko Haram.
Rundunar sojin ta bayyana cewa ta yi nasarar gamawa da mayakan Boko Haram da dama tare da kwato mutane da dama da suka yi garkuwa da su, tare da ruguje inda suke kera makaman su.
Mataimakin shugaban rundunar Operation Lafiya Dole Kanal Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau, inda ya ce rundunar tayi nasarar gamawa da wata babbar matattarar su da aka fi sani da Sabilul Huda.
An dai gano matattarar ne a tsakiyar dajin Sambisa, inda kuma aka tabbatar da cewa nan ne matattarar mayakan na Boko Haram a ciki dajin na Sambisa yayin da rundunar ta ce ta samu wannan nasara ne da taimakon rundunar sojin saman kasar nan.
Rundunar ta kuma kara da cewa ta yi nasarar ceto mata 19 da yara 27 a yayin barin wutar.
Tun a ranar 4 ga watan Fabrairun da muke ciki ne rundunar ta bayyana cewa ta gama da kungiyar ta Boko haram a dadin kasar nan.