Kiwon Lafiya
Rundunar Sojin Najeriya za ta hada kai da Mafarauta da yan Vigilante don inganta tsaro
Rundunar Sojin kasar nan ta baiwa gamayyar kungiyoyin sa-kai na Mafarauta da na Vigilante a Jihar Borno tabbacin cewa a shirye take ta hada hannu da su don kawo karshen matsalolin tsaron da suka addabin yankin Arewa maso gabashin kasar nan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayar, ya ce mai rikon mukamin Kwamandan rundunar ta bakwai Birgediya Janar Abdulmalik Biu ne ya bada tabbacin, lokacin da ya gana da ‘yan kungiyar karkashin shugabanta Alhaji Maigana Maidarma.
Janar Abdulmalik Biu ya ce kwarewar da mafarautan ke da shi gami da yadda suka san Surkukin yankin zai taimaka gaya wajen kawo ayyukan mayakan Boko Haram a yankin baki-daya.
Sannan ya shawarcesu su rika gaggauta bayar da bayanai da zarar sun samu game da yadda ‘yan ta’addan ke gudanar da harkokinsu a yankin, don ganin an dawo da zaman lafiya da wanzuwar arziki kamar da.
Da yake jawabi, shugaban gamayyar kungiyoyin tsaron Maigana Maidarma bayyana hadin kansu ya yi ga hukumomin tsaron kasar nan, sannan ya kuma shaida cewa suna fuskantar kalubalen da suka hadar da na Motocin hawa da kuma Makamai.