Labarai
Rundunar Sojin Sama ta gargadi yan ta’addan da suka addabi Zamfara

Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta gargadi ƴan ta’addan da ke addabar jihohin Zamfara da Katsina da Kebbi da Sokoto da su gaggauta barin maboyar su tare da mika kan su ko kuma su fuskanci matsanancin farmaki daga jiragen yaki.
Wannan gargadi ya zo ne kasa da mako guda bayan rundunar ta yi luguden wuta ta sama kan sansanonin ƴan ta’adda a wasu kauyuka na jihar Zamfara.
Da yake jawabi a jiya Laraba yayin gudanar da Faretin soji na musamman a birnin tarayya Abuja, Shugaban Sojin Saman, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ce dakarun za su ci gaba da binciko maboyar waɗannan miyagun mutane tare da kawar da su baki ɗaya.
Haka kuma, ya ce, rundunar za ta ci gaba da kare sararin samaniyar kasar tare da ba da gudummowa da hadin gwiwar jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi al’umma.
You must be logged in to post a comment Login