Labarai
Rundunar Sojin sama ta dauki alhakin harin da aka kai Rukuba

Shugaban rundunar sojin saman Nijeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ya tabbatar da daukar alhakin harin da aka kai kauyen Rukuba na karamar hukumar Doma a jihar Nassarawa a bara, yana mai cewa dakarun rundunar sun kai harin ne bisa kuskure.
Harin dai ya rutsa da wasu makiyaya ne dake tafe da daruruwan dabbobin su a kan hanyar su ta sauya matsugunni bayan da gwamnatin jihar Benue ta ayyana dokar hana kiwo a dazukan jihar.
Kimanin mutane 40 ne suka rasa rayukan su yayin harin bom din da sojoji suka kai bisa kuskure tun a farkon watan janairun bara.
Wannan dai na zuwa ne makonni kalilan bayan da rundunar ta dauki alhakin irin wannan hari da dakarun ta suka kai kauyen tudun biri a jihar Kaduna.
You must be logged in to post a comment Login