Connect with us

Labarai

Rundunar Sojoji ta ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da halaka ’yan ta’adda biyar

Published

on

Rundunar Sojojin kasar nan ta Operation FANSAN YAMMA, ta ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su, tare da halaka ’yan ta’adda biyar yayin wasu atisaye da ta gudanar a jihohin Zamfara da Katsina.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya tabbatar da hakan, ya na mai cewa dakarun za su ci gaba da kai hare-hare domin murƙushe ta’addanci tare da dawo da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Yamma.

Haka kuma, ya ce, an ceto mutane 31 din ne a yankin Bagega zuwa Kawaye da ke ƙaramar Hukumar Anka ta jihar Zamfara bayan jefa bama-bamai daga jiragen yaƙi a maɓoyar ’yan ta’addan a Dajin Bagega.

Haka kuma, ya kara da cewa, waɗanda aka ceto sun shafe tsawon makonni da dama a tsare, kuma ’yan asalin ƙananan hukumomin Maga da Gummi da Zuru da Wasugu da Bukuyyum da kuma Anka ne da ke jihohin Zamfara da Sokoto.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!