Labarai
INEC ta gargadi jam’iyyun siyasa kan yuwuwar soke zabukan fidda gwani

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da cewa duk wani zaɓen fidda gwani da aka gudanar bayan wa’adin 30 ga Mayu da hukumar ta sanya ba mai inganci ba ne , sai dai idan wata babbar kotu ta soke hukuncin da Babbar Kotun tarayya ta yanke kan lamarin.
Kwamishinan hukumar na Ƙasa kuma shugaban Kwamitin yaɗa labarai da Ilimantar da masu zaɓe, Muhammad Kudu Haruna ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da jaridar Punch
Muhammad Kudu ya ce jam’iyyun siyasa su ci gaba da bin tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2026 har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan ƙarar da INEC ta ɗaukaka.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddamar shari’a kan jadawalin zaɓukan fidda gwani da gabatar da sunayen ’yan takara gabanin babban zaɓen 2027.
A baya babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari’a Muhammad Umar ta soke wasu sassa na ƙa’idojin zaɓe da jadawalin da INEC ta tsara domin gudanar da zaɓen 2027.
A hukuncin da ta yanke kan ƙarar da jam’iyyar Youth Party ta shigar, kotun ta ce INEC ba ta da ikon rage wa’adin da sashe na 29(1) na dokar zaɓe ta 2026 ya tanadar na gabatar da rajistar mambobin jam’iyya da bayanan ’yan takara.
Kotun ta kuma bayyana cewa INEC ba za ta iya takaita wa’adin da doka ta tanada ba, tana mai cewa hukumar ta wuce iyakar ikon da dokar ta ba ta.
Daga bisani, INEC ta ɗaukaka ƙara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin.
You must be logged in to post a comment Login