Connect with us

Labarai

A saki ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno – MDD

Published

on

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a saki ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno  a hare-haren da suka faru a jihohin.

Mai kula da ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya da na jin ƙai a kasar nan  Mohamed Malick Fall,  ne ya bayyana hakan a ganawarsa da tawagar Cibiyar Kula da Tsaron Makarantu ta Ƙasa a birnin tarraya Abuja, ƙarƙashin jagorancin Dakta Samuel Umanah.

A cewarsa, bai kamata a ci gaba da zuba ido ana ganin matsalar tsaro na  ci gaba da yiwa makarantu barazana a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa irin waɗannan hare-hare na kawo cikas ga ilimi da kariyar yara.

Ya ce makarantu ya kamata su kasance wuraren ilimi masu aminci, ba wuraren tsoro ba, yana mai jaddada cewa bai kamata yara su zama abin hari ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!