Connect with us

Labaran Kano

Rundunar ‘Yan sanda a Kano zata kara kaimi kan yaki da aikata laifuka

Published

on

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da kuma al’umma, domin tabbatar da zaman lafiya da magance matsalolin tsaro a jihar.

Mataimakin Kwamandan ’yan sandan Ofishin ’yan sanda na yankin Sharada, DSP Muhammad Lawan, ne ya bayyana haka a wani taro da kwamitin tsaro na yankin Rinji Ja’en, da ke unguwar Sharada a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano.

DSP Muhammad Lawan ya ƙara da cewa wajibi ne iyaye su ɗauki matakan sanya ido kan ’ya’yansu tun daga matakin farko, domin hana su shiga aikata munanan ayyuka da ka iya janyo matsalar tsaro.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar Vigilanti ta jihar Kano, Shehu Rabi’u, ya ce za su ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankunan da suke aiki, duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

Shi ma mai unguwar Rinji Ja’en, Muhammad Sani Rinji, ya ce dalilin shirya taron ya samo asali ne daga yadda wasu matasa ke sayarwa da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi a yankin, baya ga yawaitar rahotannin satar kayayyaki da sauran matsalolin da suka shafi tarbiyyar al’umma.

Taron ya samu halartar jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban, da malaman addini, da sauran al’umma, inda mahalarta suka cimma matsayar haɗa kai da yin aiki tare domin tsaftace yankin Rinji Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!