Connect with us

Labaran Kano

Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci ta fara binciken wani da ake zargi da daukar ma’aikatan bogi a Kano

Published

on

Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta fara bincike tare da kama wani mutum, Adam Aliyu Yahaya, da ake zarginsa da ɗaukar ma’aikata na bogi da ba su shaidar aiki a ma’aikatun gwamnati.

 

Shugaban Hukumar, Malam Sa’idu Yahaya, ya ce zuwa yanzu sun samu takardar umarnin kotu na kada a tsare shi ko a matsa masa, amma suna jiran hukuncin kotu domin ci gaba da binciken.

 

Zuwa yanzu Hukumar ta bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da Hukumar gwamnati kuma ba jami’inta ba ne.

 

Sa’idu Yahaya ya yi kira ga jama’a cewa gwamnati ba ta karɓar kuɗi don bayar da aiki, kuma duk wanda ya bayar ko aka ba shi kuɗi ya aikata laifi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!