Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda ta koka kan tsaiko da rashin daidaito tsakanin su da Lauyoyi kan aiwatar da court order ga wadanda ake zargi

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana damuwa kan koma-baya da tsaiko da ake samu tsakanin jami’an ‘yan sanda da lauyoyi wajen aiwatar da umarnin kotu (court orders).
Barrister CSP Nura Sa’idu, mai kula da bangaren shari’a na Shiyya ta Daya (Zone 1) a Kano, ne ya yi wannan jawabi a wani taro da kungiyar Isa Wali Empowerment Initiative suka shirya domin samar da daidaito da ingantaccen hadin kai.
CSP Nura Sa’idu ya ce rashin daidaito da rashin fahimtar juna a ayyukan ‘yan sanda da lauyoyi na haifar da tsaiko wajen aiwatar da umarnin kotu, lamarin da zai iya kawo tangarda a tsarin shari’a da kuma kawo rashin zaman lafiya.
Ya kara da cewa dole ne a fayyace iyakokin aikin kowa domin gujewa tsangwama da rikice-rikice da zasu iya shafar gudanarwar shari’a.
Idan aka ci gaba da rashin daidaito game da batun court order, ba za a samu zaman lafiya ba,” in ji Barr. CSP Nura, wanda ya bukaci a gina tsarin hulda da zai sanya kowa yana aikin da ya dace ba tare da takura wa dayan bangaren ba.
A nata bangaren, Hajiya Aisha Isa Yusuf Manajan Shirye-shirye ta kungiyar Partners West African Nigeria ta bayyana cewa manufar taron ita ce tabbatar da adalci ga al’umma tun daga matakin farko a police station. Aisha ta ce an yi nufin kafa tsarin da zai samar da lauya mai bayar da tallafin shari’a kyauta a ofisoshin ‘yan sanda, don rage yawan shigar da kara marasa nauyi zuwa gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login