Kiwon Lafiya
Rundunar yan sanda ta mayar da jami’anta da ake zargin wajen kashe shugaban boko haram
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta mayar da wasu jami’an ‘yan sanda biyar da ake zargi da hannu wajen kashe jagoran da ya kafa kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf, lokacin da yake hannun su bakin aikin su.
Kakakin hukumar kula da harkokin ‘yan sandan na kasa Ikechukwu Ani ne ya tabbatar da mayar da jami’an yan sandan bakin aikin su, a wata sanarwa da ya fitar.
Wani masani kan harkoki tsaro na cibiyar nazarin harkokin kasa-da-kasa Amaechi Nwakolo yace mayar da jami’an ‘yan sandan bakin aikin su abin a yaba ne, la’akari da irin gudun mowar suka bayar.
Ana tuhumar yan sandan da aikata ta’addanci, kisa ba bisa ka’ida ba, lokacin da rundunar ke tsaka da gudanar da ayyukan ta na tayar da hankulan jama’a a Maiduguri cikin watan Yulin shekarar 2009.
Yayin arangamar tsakanin jami’an tsaro da ‘yan tada kayar bayan, mayakan Boko Haram kimanin dari takwas ne aka kashe a lokacin, wanda yayi sanadiyyar fusata kungiyar har tayi sanadiyyar raba mutane dubu ashirin da rayukan su, yayinda sama da miliyan biyu kuma suka rasa matsugunan su.