Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta kori jami’anta kan zargin harbe farar hula

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da daukar matakin sallama da gurfanar da wasu jami’anta da ke da hannu a harbin da ya yi sanadiyyar mutuwar Mista Mene Ogidi a Effurun, Jihar Delta, ranar 26 ga Afrilu, 2026.

 

 

Ta ce an dauki matakin ne bayan umarnin Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa, IGP Olatunji Rilwan Disu, wanda ya sa aka janye jami’an daga Delta zuwa hedikwata da ke Abuja domin gudanar da bincike cikin gaggawa.

A cewar rundunar, binciken kwamitin ladabtarwa ya tabbatar da cewa ASP Nuhu Usman ya karya dokar Force Order 237 da sauran ka’idojin amfani da bindiga. Ta bayyana cewa abin da jami’in ya aikata ya saba doka, ya nuna rashin kwarewa tare da cin amanar aikin kare rayuka da tabbatar da doka, lamarin da ya sa aka ba da shawarar sallamarsa tare da sauran wadanda aka samu da laifi.

Rundunar ta ce IGP ya amince da shawarar kwamitin tare da tura ta zuwa Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda domin tabbatarwa bisa ka’ida. Ta kara da cewa bayan kammala matakan gudanarwa za a mika jami’an ga hukumomin shari’a domin gurfanar da su. Haka kuma, rundunar ta mika ta’aziyya ga iyalan mamacin tare da jaddada cewa ba za ta lamunci kisa ba tare da bin doka ba ko cin zarafin iko.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!