Connect with us

Labarai

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Published

on

Kotun Koli ta sanya ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, domin yanke hukunci kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC). Tun da farko kotun ta ajiye hukunci bayan kammala sauraren karar, lamarin da ya sa bangaren jam’iyyar ya rubuta wa Babban Alkalin Najeriya yana neman a gaggauta yanke hukuncin saboda lokaci na kurewa.

 

Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne ya saurari karar, inda bangaren Sanata David Mark ke kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta umarci a ci gaba da zama yadda ake ciki. Mark ya ce rikicin cikin gida ne na jam’iyya wanda kotu ba ta da hurumin shiga cikinsa.

 

Bangaren Mark ya bayyana cewa idan ba a yanke hukunci cikin gaggawa ba, ADC na fuskantar barazanar rasa damar shiga zaben shekarar 2027. Sun kuma yi zargin cewa INEC ta cire amincewa da shugabancin jam’iyyar, abin da ya bar ta babu sahihin jagoranci a halin yanzu. Sai dai wadanda ake kara sun bukaci Kotun Koli ta yi watsi da karar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!