Labarai
NNPCL ya miƙa wa Asusun Tarayya sama da tiriliyan 7 tsakanin Janairu da Yulin 2026

Kamfanin Mai na kasa , NNPCL ya ce ya miƙa wa Asusun Tarayya na ƙasar nan sama da naira tiriliyan 7, tsakanin watan Janairu da Yuli na shekarar 2026.
NNPC ya bayyana hakan ne a cikin rahoton ayyukansa na kuɗi da na samar da man fetur na watan Yuli, wanda aka fitar a yau Laraba.
Kamfanin ya ce ya samu kuɗaɗen shiga na naira tiriliyan 3.09, yayin da ribarsa bayan biyan haraji ta kai naira biliyan 279 a lokacin.
NNPC ya ce an kuma samu raguwar samar da mai sakamakon matsalolin aiki a wasu wuraren hakar mai, ciki har da lalacewar wasu cibiyoyi, rashin kayan aiki, matsalolin bututun mai da kuma wasu ƙalubalen samar da mai.
Haka kuma, raguwar samarwar ta yi tasiri kan yawan ɗanyen man da da aka sayar, wanda ya kai ganga miliyan 22.53 a watan Yuli, idan aka kwatanta da ganga miliyan 28.23 a watan Yuni.
You must be logged in to post a comment Login