Manyan Labarai
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kwato Shanu sittin
Rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina, ta sanar da kashe dan garkuwa da mutane, gudan daya tare da kwato shanu sittin.
Rundunar ta sanar da kubutar da Shanu sittin da Tumaki tamanin a wani kwantan bauna da tayi wa ‘yan garkuwa da mutane da suka farwa Kauyen Karo da Garangamawa a karamar hukumar Dutsin ma ,ta jihar.
A wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar Sufeto Gambo Isah, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, ta tabbatar dacewa rundunar ta samu rahoton cewar ‘yan garkuwa da mutane dauke da bindigogi kirar AK 47, sun shiga kauyukan da karfe biyun daren jiya Laraba, tare da kai hari kan garuruwan.
Labarai masu alaka.
An kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Katsina
Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina
Sanarwar ta kara dacewa Jim kadan bayan samun labarin Babban jami’in ‘yan sanda na Dutsinma , ya umarci tawagar musamman ta Operation Puff Adder, tare da ‘yan sintiri na Unguwar Bara, wajen kai samame ga yan ta’addar.
A harin kwantan baunan, jami’an sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan wanda a ciki suka samu nasarar kashe daya daga cikin ‘yan garkuwa da mutane tare da kwato shanu sittin da tumakai tamanin.Haka kuma tawagar ta cigaba da sintiri da duba mabuya daban -daban a cikin dajin, don neman wanda suka tsere da harbi a jikin su ,tare da kwato makaman su ,tare da fadada bincike.
You must be logged in to post a comment Login