Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta kama matasa 83 da ake zargi da kwacen waya a Kano
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama matasa 83 da ta ke zargi da aikata fashi da makami a lokacin bukukuwan sallah karama
- Matasan da aka kama an kamasu ne a cikin lunguna da sako na Jihar Kano
- Yayin da wasunsu aka kamasu suna siyar da miyagun kwayoyi
- Rundunar ‘yan sandan ta ce ‘da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu’
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama matasa 83 da ta ke zargi da aikata fashi da makami a lokacin bukukuwan sallah karama.
Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan, ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio a daren jiya.
Wanda ya ce ‘matasan da aka kama an kamasu ne a cikin lunguna da sako na Jihar Kano, wadanda yawancinsu aka kamasu da makamai a hannunsu, suna yunkurin yiwa mutane fashi na wayar hannu’.
‘Yayin da wasunsu aka kamasu suna siyar da miyagun kwayoyi ga ire-iren matasan da ake zargin da fashi da makamin’.
‘Haka zalika rundunar ta samu nasarar karbar kayayyaki a hannunsu da suka hadar da wayoyin hannun, jakakkunan mata, da na’u’rar kwamfuta a hannun matasan’.
Sai dai rundunar yan sandan ta ce, da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login