Kiwon Lafiya
Rundunar yan sandan tayi bayani kan yadda Dino Melaye yayi yunkurin kubucewa
Rundunar yan sandan kasar nan ta yi bayani dalla-dalla kan yadda Sanatan kogi ta Tsakiya Sanata Dino Melaye ya yi yunkurin kubucewa daga hannun su da yammacin jiya Talata.
A cewar rundunar yayin hakan ne domin kaucewa aikewa da shi garin Lokoja, inda kuma ta bada tabbacin cewar ko mai rintsi sai ta iza keyar sa zuwa garin Lokoja inda zai fuskanci hukunci kan zargin kisan kai.
Da yammacin jiya ne dai aka dauki senator Dino Melaye zuwa asibiti a birnin tarayya Abuja bayan da aka yi zargin cewar kafar sa ta karye bayan da yayi yunkurin dirgowa daga motar yan sanda.
An dai jiyo Dino Melaye na cewar shi fa ba za a kai shi garin Lokoja domin gurfanar da shi ba, inda ya ce ya na tabbacin ba za yi masa adalci ba ya kuma bukaci koma me zai faru ya faru a birnin tarayya Abuja amma ba a Lokoja ba.
Rahotanni na nuni da cewa Dino Melaye na da tsatsatsamar alakar siyasa da gwamnan Kogi Yahya Bello lamarin da ya sanya yaki amincewa da a damka shi a hannun gwamnan.
A daren Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun rundunar yan sandan kasar nan Jimoh Mashood ya fitar da wata sanarwa inda ya ce rundunar ta kuma damke Dino Melaye kuma za su aike dashi garin Lokoja domin fuskantar shari’a