Labarai
Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara da hadin gwiwar kwamitin zaman lafiya na gwamnatin Jihar sun samu nasarar ceto mutane 11 da masu garkuwa da mutane suka sace a Jihar.
Mai magana da yawun rundunar Muhammad Shehu ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Gusau.
Muhammad Shehu ya ce an sace mutanen ne a ranar juma’ar da ta gabata, 4 ga wannan wata na Yuni da muke ciki, a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe.
Ya kara da cewa kafin sada mutanen da aka ceto da iyalansu sai da aka duba lafiyarsu a asibiti don tabbatar da koshin lafiyarsu.
You must be logged in to post a comment Login