Kiwon Lafiya
Rundunar yan sandar jihar Kano ta kama mataimakin gwamnan Kano
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama Mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo da shugaban karamar hukumar Nasarawa Lamin Sani saboda zargin kawo hargitsi a yayin da ake kokarin tattara sakamakon zabe.
Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin su da kai hari ofishin tattara sakamakon zabe da misalin karfe 1 da minti 30 tare da ‘yan bangar siyasa wanda suka sanya tsoro a zukatan mutane kafin jami’an tsaro su kawo dauki.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kawo yanzu ana dakwan karamar hukumar Nassarawa kawo yanzu bayan da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 43.
Jami’an ‘yan sandan dai sun dauke wanda ake zargin zuwa shalkwatar rundunar dake Bompai ana Kano.