Labarai
Rundunar ‘yansanda ta gano wurin kera makamai a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta gano wani wurin da ake ƙera bindigu ba bisa ka’ida ba a garin Potiskum tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a lamarin.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun kai samame ne a wani garejin gyaran karafa da ke Tasha Adua a kan titin Danchuwa bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargin suna kera bindigogin gargajiya da sauran makamai.
Rundunar ta ce ta kwato bindigogi da aka kera, da wasu sassan bindigogi da kayan aikin da ake amfani da su wajen kera makaman.
Haka zalika, ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin da kuma masu sayen makaman.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, Usman Kanfani Jibrin, ya umarci jami’an da ke gudanar da binciken su fadada bincike domin gano sauran wuraren da ake kera makamai ba bisa ka’ida ba a yankin.
You must be logged in to post a comment Login