Labarai
Sojoji sun hallaka kwamandojin ‘yan ta’adda da karin wasu 50 a Najeriya

Rundunar Sojin kasar nan ta tabbatar da hallaka wasu manyan kwamandojin ’yan ta’adda tare da sama da mayaƙa 50 a hare-haren sama da aka kai a yankin Tafkin Chadi ƙarƙashin aikin Operation Hadin Kai.
Majiyoyin tsaro, sun tabbatar kai harin a ranar 31 ga Mayu a yankunan Kirta da Arina Ciki bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ’yan ta’addan a wuraren.
Rahoton ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai Khalifa Umar, wani fitaccen mamba a majalisar Shura ta ’yan ta’addan, da wasu kwamandoji biyu masu suna Abdallah da Abduljalil.
Baya ga kashe mayaƙan, hare-haren sun lalata cibiyoyin ajiya, wuraren samar da kayayyaki da sauran muhimman gine-ginen da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa matsin lambar hare-haren sama ya sa da dama daga cikin ’yan ta’addan suka bar maboyarsu da ke tsibiran Tafkin Chadi zuwa wasu wurare da suka fi bayyana a doron ƙasa.
Haka kuma, jami’an tsaro sun ce duk da cewa yanayin tsaro a yankin yana bunƙasa, har yanzu ana ci gaba da sanya ido tare da ɗaukar matakan kariya.
You must be logged in to post a comment Login