Connect with us

Labarai

Abuja: Yan Sanda sun ƙwato bindigogi 2 da harsasai daga hannun yan bindiga

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta ƙwato bindigogi 2 da harsasai daga wata maboyar ‘yan bindiga da ke Dajin Madam, bayan wani sumame da jami’anta suka kai.

 

wannan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar 5 ga Agustan 2026.

 

Sanarwar ta bayyana cewa binciken ya biyo bayan kama wasu mutane huɗu da ake zargi da safarar makamai, alburusai da miyagun ƙwayoyi ga ‘yan bindiga. Ta ce bayanan da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayar ne suka kai jami’an zuwa maboyar da ke Dajin Madam tsakanin Jihohin Filato da Bauchi.

 

Ya ce, Binciken ya kuma nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin yana karɓar makamai daga wani mutum tare da kai wa wani shugaban ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, wanda ake kyautata zaton yana buya a wani daji da ke Jihar Katsina.

 

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke sauran mambobin ƙungiyar, ƙwato ƙarin makamai da kuma gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!