Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Sabon rikici ya ɓarke a Kannywood bayan kama wani jarumi

Published

on

Jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood sun fara mayar da raddi kan zargin kama wani mai mai shirya fina-finai Mu’azzamu Idi yari.

A cewar su, wannan ba wani abu bane face tsan-tsar siyasa, suna masu cewa an kama shi ne saboda akwai saɓani tsakin sa da shugaban hukumar tace fina-finan Kano Isma’il Na’abba Afakalla.

A zantawar sa da Freedom Radio Jarumi Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Na Buraska ya ce, babu wata doka da Mu’azzamun ya karya wadda zata bada damar kama shi.

Ya ƙara da cewa, dama tun da Mu’azzamun ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, shugaban hukumar Isma’il Na’abba Afakalla ya yi barazanar kama shi da ɗaure shi, har ma ya ce masa, su ne da muƙami a yanzu don haka yadda suka ga dama zasu yi.

Labarai masu alaka:

Kannywood ta fara mayar da martani kan matakin hana sanya Fina-fanai a manhajar Youtube

Rashin sanya jarumai a guraban da suka dace zai durkusar da Kannywood – Abdul M. Sheriff

Shi ma jarumi kuma mai shirya fina-finai Falalu .A. Ɗorayi a wani jawabi da ya wallafa a shafin sa na Facebook ya zargi hukumar da cin zarafi, tozarci da kuma zalintar Mu’azzamu idi Yarin.

Ta cikin jawabin da ya wallafa, Falalu .A. Dorayi ya ce, kamata ya yi ace ana sasanta irin waɗannan matsaloli ta hanyar maslaha, amma ba kamawa ko ɗauri ba.

Amma da ya ke mayar da martani shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’I ta jihar Kano Ismai’l Na’abba Afakalla ya ce, hukumar sa na kan doka.

A cewar sa, Mua’zzamu Idi Yari ya take dokokin hukumar na ɗaukar fim ba tare da izini ba, a don haka aka kama shi don girbar abinda ya shuka.

Ko da aka tambaye shi a kan zargin cewa ya kama Idi yari ne saboda akwai rashin jituwa a tsakanin su, sai ya ce babu wani abu mai kama da haka iyaka dai an kama shi ne don karɓar hukuncin laifin da ya aikata kawai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!