Connect with us

Labarai

Sai an biya kudin fansa kafin sakin Marayu – ‘Yan bindiga

Published

on

‘Yan bindigar da suka sace yara 7 ciki har da wani maigadi a gidan marayu na ƙauyen Naharati dake Abuja, sun nemi a biyasu naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Sai dai mahukuntan dake kula da gidan marayun, sun ce basu da kudi, ya yin da suke ikirarin cewa  hatta ciyarwa da kuma suturar da marayun ke sawa wasu kungiyoyin jinkai ne ke tallafawa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, kawo yanzu rundunar yansandan Abuja ba ta ce uffan ba.

A ranar Asabar da daddare ne, ‘yanbindigar ɗauke da makamai suka kutsa cikin gidan marayun da ke ƙauyen Naharati da ke wajen birnin tarayyar sannan suka yi awon gaba da yaran.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!