Labarai
Sakacin iyaye ne ke kawo rashin tarbiyya -Dakta Zahra’u
Gwamnatin jihar kano ta danganta matsalolin da ake samu a wannan zamani da tsantsar rashin tarbiyyar da iyaye ke gaza baiwa ‘ya’yansu da kuma yawaitar jefar da yara ake yi.
Kwamishiniyar mata da walawalar jama’a ta jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Radiyo freedom, wanda ya mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi tabarbarewar tarbiyya a wannan lokaci.
Dakta Zahra’u ta ce, wajibi ne iyaye su tashi tsaye wajen inganta tarbiyyar ‘ya’yansu don samun raguwar matsalolin da ake fuskanta a gidajen aure.
Ta kuma kara da cewa, dawo wa kan tafarkin addini zai ragewa iyaye mata matsalolin da suke fuskanta a zamantakewar aure.
Kwamishinyar ta yi kira ga masu hannu da shuni da sarakuna da kuma sauran jama’a da su hada hannu wajen tallafawa gwamnati don ganin an inganta rayuwar mata da kuma kananan yara a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login