Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Sakamakon jarrabawar ɗaliban da suka yi daga baya ya fito – JAMB

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun ƙasar nan JAMB ta saki sakamakon jarabbawar ɗaliban da suka rubuta a ranar Juma’ar da suka gabata.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dr. Fabian Benjamin ya fitar a Abuja.

Ya ce, jarrabawr an gudanar da ita a wasu cibiyoyi da hukumar ta zaɓa a fadin kasar nan, ga ɗaliban da basu samu damar rubuta jarrabawar da aka yi a watannin ba.

Sanarwar ta buƙaci daliban da su duba shafin internet na hukumar don fito da sakamakon su.

Sama da .ɗalibai dubu goma sha bakawai ne suka rubuta jarrabawar a ranar juma’a, sakamakon matsalolin da suka fuskanta a lokacin rubuta jarrabawar a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!