Labarai
Sakin Abduljabbar barazanar tarzoma ce a cikin al’umma – Lauyan gwamnati
Lauyan gwamnati Barista Mamman Lawal Yusufari ya ce “Kotu ta zauna wanda ake ƙara ya kawo sabbin lauyoyi, tun da sabbin zuwa ne sun buƙaci a basu kwafin shari’a kuma mun amince, amma kuma batun beli ne muka ki amincewa”.
“Doka ba ta ba da damar a bada beli ga mai laifi irin na Abduljabbar ba, domin kuwa sakin sa zai iya tayar ta tarzoma a cikin al’umma, kuma ma ba su da ƙwaƙƙwaran dalilin na ba da belin” in ji Yusufari.
Wannan dai ya biyo ayan zaman babbar kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a ƙofar kudu ƙarkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola.
A zaman kotun na ranar Alhamis Lauyan gwamnati tare da mataimakansa sun gabatar da kawunansu ƙarkashin babban lauya Suraj sa’ida.
Haka shi ma sabon lauyan Malamin wato Umar Muhammad ya gabatar da kan sa da sauran abokan aiki.
Ko da kotu ta waiwayeshi nan ta ke ya bayyana cewa, “Tun da yau muka fara zuwa muna rokon kotu ta ba mu kwafin shari’ar da aka yi a baya domin mu nazarci yadda shari’ar ta ke, mu kuma san daga ina za mu ɗora, tun da mun gabatar da kan mu”.
“hana beli da kotu ta yi yayi daidai domin hurumin ta ne, kuma muna kyautata zaton za ta yi adalci” in ji lauyan wanda ake ƙara.
Har ma ya bukaci masu gabatar da kara su kawo shaidunsu gaban Kotu.
Kotun ta ji bayanin sa ta kuma waiwayi lauyan gwamnati, inda ya ce “Ba mu da suka a kan roƙon ba da kwafin shari’ar amma batun shaidu a halin yanzu suna gaban kotun” in ji lauyan gwamnati.
Kotu ta kuma bayyanawa lauyoyin Malam Abduljabbar cewa, tuni suka aike da takardar shari’ar amma lauyan malamin ya ce ba su aka bai wa ba.
Haka kuma lauyan na Abduljabbar ya buƙaci a ba su belin wanda suke karewa, kuma nan ta ke lauyan gwamnati ya yi suka.
Daga ƙarshe Kotu ta yi dogon nazari kuma taki amincewa da bada belin bisa wasu hujjoji.
Shi ma lauyan gwamnati Barista Mamman Lawal Yusufari ya ce “Kotu ta zauna wanda ake ƙara ya kawo sabbin lauyoyi, tun da sabbin zuwa ne sun buƙaci a basu kwafin shari’a kuma mun amince, amma kuma batun beli ne muka ki amincewa”.
“Doka ba ta ba da damar a bada beli ga mai laifi irin na Abduljabbar ba, domin kuwa sakin sa zai iya tayar ta tarzoma a cikin al’umma, kuma ma ba su da ƙwaƙƙwaran dalilin na ba da belin” in ji Yusufari.
Sai dai daga karshe kotu ta dage ci gaba da saurar shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login