Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sallah : Yadda kayan miya da man gyada suka yi tashin gwauron zabi a Kano

Published

on

Ya yin da ake jajibi ga sallah don gudanar da bikin babbar sallah, wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ziyarci wasu daga cikin kasuwannin da ke nan birnin Kano don ganin yadda hada-hada ke wakana.

Sallar layya ko sallah babba lokaci ne da akasari al’ummar musulmi ke gudanar da ibadar layya domin sauke nauyin da All.. ya daura musu matukar suna da hali.

Kamar yadda aka saba gani a lokaci irin wannan na babbar sallah jama’a kan shiga kasuwanni domin gudanar da saye-saye musamman kayan miya da na kanshi da mai da sauransu.

Man gyada kamar sauran kayayyakin hadi abune da ke da matukar muhimmanci sakamakon amfaninsa a lokaci irin wannan.

Sai dai a ziyarar da muka kai kasuwar Rimi mun gano cewa farashin na Man gyada yayi tashin gwauron zabi kamar yadda wadannan mutane da suka zo sayayya kasuwar suka bayyana cewar sun yi mamakin yadda man ya tashi

Alhaji Awwal Sani shi ne shugaban ‘yan kasuwa da ke sayar da man gyada a kasuwar ta Rimi ya yi karin haske kan makasudin hauhawar farashin man a wannan lokaci na sallah kasancewar an saba ganin irin wannan haka sai dai kawai addu’ar neman sauki.

Yace suma firashin ne ya karu daga inda suke sarowa akan ya zama tilata suka firashin man gyadar.

A bangaren masu sayar da kayan miya a kasuwar Sharada  kuwa mafi yawa na masu wadanda suka zo yin cefane a kaswaur sun koka kan yadda aka samu Karin farashi.

Freedom rediyo ta kuma zanta da Alhaji Naiya Sharada wanda shi ne shugaban masu sai da kayan miya a kasuwar ta Sharada, ya ce kayan miya sun yi tashin gwaran zabi

A wasu kasuwanni kuwa mun lura cewa akwai karancin futowar mutane ,wanda ake ganin rashin kudi da kuma yanayin annobar Covid 19 da ya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!