Kiwon Lafiya
Sama da mutum dubu 18 ne ke ɗauke da cutar tarinfuka a Kano – ma’aikatar lafiya
Gwamnatin jihar kano ta ce sama da mutane dubu goma sha takwas aka gano masu ɗauke da cutar tarinfuka.
Babban jami’i mai kula da bangaren yaƙi da cutar tarin fuka da kuturta a ma’aikatar lafiya ta Kano Dakta Ibrahim Aliyu Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da freedom radio a wani ɓangare na bikin ranar yaƙi da cutar tarinfuka da ake gudanarwa.
Dakta Ibrahim Aliyu ya kuma ce “Cutar tarinfuka cuta ce da ke yaduwa daga wani zuwa wani ta yadda take shafar huhu kai tsaye wanda hakan ke haddasa matsanancin tari”.
“Illolin cutar kan tsallaka ga sauran sassan jiki da suka haɗa da ƙoda, Hanta, ƙwaƙwalwa da kuma ƙashin baya.”
Ya kuma ce ana gane alamomin cutar tarinfuka ne ta hanyar yawan ciwon kai, gumin dare da kuma yawan jin kasala.
Majalisar ɗinkin duniya ce dai ta ware duk ranar 24 ga watan maris ɗin kowace shekara a matsayin ranar wayar da kan mutane kan cutar tarinfuka.
Taken bikin ranar na bana shi ne ƙara saka tallafi don kawo ƙarshen cutar a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login